Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya jagoranci taron bankwana na majalisar kula da tattalin arziki ta ƙasa a yau Alhamis.
An gudanar da taron ne a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
Manyan jami’an gwamnati ciki har da gwamnoni da kuma ministoci ne suka halarci taron majalisar na bankwana.