Tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya mayar da martani ga hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ta tabbatar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Wata sanarwa da kansa ya sanya wa hannu, wacce ofishin yada labaransa ya fitar, ta bayyana hukuncin PEPT a matsayin nasara ga dimokuradiyya da bin doka da oda.
“Hukuncin babbar nasara ce ga dimokuradiyyar tsarin mulkin Najeriya da kuma bin doka,” in ji shi.
A cewar Osinbajo, wanda ya tsaya takara a jam’iyyar All Progressives Congress, zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, kuma ya zo na uku bayan Tinubu da tsohon ministan sufuri, Chibuike Amaechi, an kara karfafa tsarin dimokuradiyya a kasar nan.
Ya ce kuma abin farin ciki ne ga dimokuradiyya kasancewar dukkan jam’iyyu da aminci sun bi tsarin zabe kamar yadda doka ta tanada tare da dogaro da bangaren shari’a idan aka samu sabani.
Da yake taya Tinubu, Kashim Shettima, da APC, Najeriya a yanzu “tana bukatar dukkan mu mu yi aiki tare don magance kalubalen da muke fuskanta da kuma samar da ci gaba mai girma na kasarmu.”


