Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kammala zaman tattaunawa da masu ruwa da tsaki da wakilai na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.
Mai magana da yawun Mista Osinbajo, Laolu Akande, a wata sanarwa a ranar Alhamis a Abuja, ya ce mataimakin shugaban kasar ya rufe shawarwarin da ya kai jihohin Benue da Legas a ranar Laraba.
Mataimakin shugaban kasan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 a kafar talabijin da kuma ta yanar gizo a karkashin jam’iyyar APC.
“Na yi imanin cewa, dalilin da ya sa Allah Madaukakin Sarki ya ba ni wadannan abubuwan da suka faru, da wadannan bayanai, da kuma wadannan damammaki, shi ne, dole ne a yi amfani da su wajen amfani da kasarmu da manyan al’ummarta,” in ji Osinbajo a cewar Daily Nigerian.