Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya kai ziyarar ta’aziyya gidan su Hanifa, yarinyar nan ‘yar shekara biyar da a ke zargin mai makarantarsu ya hallaka ta a Kano.
Osinbajo ya kasance wani babban jami’in gwamnati, kuma dan siyasa da ya ziyarci iyayen yarinyar, wadda a ke shari’ar mutum uku da hannu da kisanta, bayan mai makarantar ta su Abdulmalik ya sace ta.
Yemi Osibanjo ya je Kano ne a yau Talata a matsayin babban bako a wurin taron shekara-shekara karo na 53 na kungiyar malaman da ke koyar da aikin lauya.