Ana sa ran dan wasan gaba na Napoli, Victor Osimhen zai rattaba hannu kan yarjejeniyar kwantiragin da Chelsea, in ji TEAMtalk.
An yi imanin Osimhen ya yanke shawarar barin zakarun Seria A wannan bazarar.
Dan wasan mai shekaru 25, wanda a yanzu yana da kudi kusan fam miliyan 112, amma ba zai koma wannan watan ba.
Sai dai Osimhen ya amince ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya a watan Janairu, kafin ya koma Chelsea a karshen kakar wasa ta bana.
Rahoton ya ce tsaffin ‘yan wasan Chelsea, Didier Drogba da John Obi Mikel na tuntubar Osimhen akai-akai, da fatan za su shawo kansa ya koma Blues.
Chelsea dai na sha’awar kara dan wasan gaba a mafi yawan kakar wasanni ta bana kuma tana da Osimhen a kan gaba a jerin ta.