Dan wasan gaba na Napoli Victor Osimhen, na shirin tattaunawa da Liverpool, tare da wasu kungiyoyin Premier biyu, Manchester United da Chelsea.
Masanin harkokin canja wuri Sacha Tavoloieri ne ya bayyana hakan a cikin wani sakon twitter a karshen mako.
“Victor Osimhen zai motsa a kasuwa! ManUnited, Chelsea FC da Liverpool sun shirya tarurruka tare da tawagar wanda ya fi zira kwallaye a gasar SerieA, “Tavoloieri ya wallafa a shafinsa na Twitter.
“Ya kamata a mako mai zuwa ya fayyace manufar kungiyoyin sa guda 3. Babban fifikon Osimhen shine gasar Premier.”
Osimhen ya kasance babban dan wasa a kungiyar Napoli a kakar wasan data gabata, domin ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin Seria A.
Dan wasan na Najeriya ya zura kwallaye 31 sannan ya taimaka biyar a wasanni 39 da ya buga a Napoli, wanda hakan ya sa ya zama dan wasan da ake nema.
Napoli ta kiyasta darajar Osimhen, mai shekara 24, kan fam miliyan 150.


