fidelitybank

Osimhen ya kama Maradona a tarihin Napoli

Date:

Victor Osimhen ya yi daidai da nasarar da Diego Armando Maradona ya samu na zura kwallo a Napoli bayan ya ci kwallaye uku a wasan da kungiyar ta doke Sassuolo da ci 6-1 ranar Laraba.

A cewar shahararren gidan yanar gizon kididdiga, Opta, Osimhen yanzu shine dan wasan Napoli na uku a tarihin kungiyar da ya zura kwallaye goma ko fiye da haka tsawon kaka hudu a jere.

Maradona ya samu nasarar ne tsakanin 1984 zuwa 1988.

Attila Sallustro shine dan wasa na farko da ya kafa tarihin Partenopei, tsakanin 1929/30 da 1932/33).

Osimhen ya zura kwallaye 10 a wasanni 24 na gasar a kakar wasa ta farko (2020/21).

Dan wasan ya bi shi da kwallaye 14 a wasanni 27 da ya buga a kakar wasa ta gaba.

A kakar wasan da ta wuce ya zura kwallaye 26 a wasanni 32 da ya buga.

Dan wasan mai shekaru 25 ya riga ya zura kwallaye 11 a wasanni 15 da ya buga a gasar Seria A wannan kakar.

pulse news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp