Shugaban kasar Liberia George Weah, ya ce, Victor Osimhen na Najeriya na iya lashe kyautar Ballon d’or saboda hazakar da ya nuna wajen ɗaga kofin Seria A a Italiya.
Weah a wani sakon ta ya murna da ya aikewa ɗan wasan, ya shawarci Osimhen kan ya ci-gaba da nuna jajircewa wajen cimma burinsa a duniyar tamaula.
Osimhen ne ya ja ragamar Napoli wajen daga kofin Seria A karon farkon bayan shekara 33, sannan ya kasance ɗan wasan Afirka da ya fi zura kwallaye a gasar ta Italiya tare da shafe tarihin da Weah ya kafa lokacin da ya ke bugawa AC Milan.
Tun bayan kafa wannan tarihi Osimhen ya kasance abin ake ta magana a kai da kuma hangen makoma mai kyau da galibin mutane ke yi masa a duniyar wasanni.