fidelitybank

Osimhen ne gwarzon dan wasan Serie A – Lukaku

Date:

Dan wasan gaba na Chelsea, Romelu Lukaku ya nada tauraron Napoli, Victor Osimhen, a matsayin ‘Dan wasan gaba mafi kyau’ a gasar Serie A ta Italiya a halin yanzu.

Lukaku, wanda a halin yanzu yake zaman aro a Inter Milan daga Chelsea, ya ce dole ne ya fadi gaskiya domin Osimhen ya ci wa Napoli kwallaye da dama a kakar bana.

Dan wasan na Belgium ya fadi haka ne a wata hira da tashar talabijin ta Sky Sport Italia ta Italiya ranar Lahadi.

Lukaku ya ce, “Spalletti ya yi babban aiki, dole ne mu ce.

“Su [Napoli] suna da ƙwaƙƙwaran ‘yan wasa. Na fita na ga yawancin wasanninsu. Napoli na cikin wani lokaci mai kyau. Osimhen ya zura kwallaye da yawa, Zielinski yana da kyau, Kvara [Kvaratskhelia], a hagu, Lozano ko Politano a dama.

“A gaskiya Osimhen yana da karfi. Yanzu shine mafi kyawun dan wasan gaba. Dole ne mu kasance masu gaskiya. Yana da ƙarfi kuma yana yi wa Napoli kyau sosai. Su ne na farko a cikin matsayi. Muna da girmamawa, amma ba tsoro ba.”

Lukaku zai yi fatan zai jagoranci Inter zuwa nasara idan za su kara da Napoli a gasar Seria A ranar Laraba.

naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...

Mukarraban gwamnati ba zan lamunci dabi’ar zubar da kima ta ba – Abba

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gargaɗi masu...

WAEC ta sake bude shafinta don duba jarabawar bana

Hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ta bayyana...

Indonesia za ta gina asibiti dubu biyu ga Falasɗinawa

Indonesia ta sanar da cewa za ta kafa wata...

Lauyan Sowore ya bukaci a sake shi cikin gaggawa

Lauyoyin ffitaccen ɗan gwagwarmayar nan kuma ɗan jarida, Omoyele...

Najeriya da Indiya za su haɗa kai na yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi

Hukumar hana sha da fatauncin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya,...

Jihohi 19 da za a yi kwana 9 a na ruwan sama harda Kano – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen za a shafe kwana...

Tinubu ya mika sakon ta’aziyya bisa rasuwar matar MKO Abiola

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa bisa...

Abubuwan da Kwamiti ya gano a wajen Kwamishina mai murabus na Kano

A ranar Litinin ne kwamitin binciken badaƙalar belin Danwawu,...
X whatsapp