Fitaccen dan wasan Super Eagles, Austin Jay Jay Okocha ya karfafawa Victor Osimhen kwarin gwiwar sauya sheka zuwa gasar Premier ta Ingila a wannan bazarar.
Ana alakanta Osimhen da manyan kungiyoyin Premier, Chelsea da Manchester United bayan nasarar da ya yi da Napoli na jagorantar Serie A.
Dan wasan mai shekaru 24 ya kuma nuna sha’awarsa ta taka leda a gasar ta Ingila nan gaba.
Okocha ya yarda cewa yin wasa a gasar Premier zai dace da Osimhen.
“To ina nufin ya yi kyau, yana da kyau sosai,” Okocha ya shaida wa BBC.
“Kuma ina ganin ya cancanci yabon da yake samu, amma abin da ya dace a gare shi shi ne ya taka leda a gasar Premier wanda shi ma ya bayyana.”
Osimhen ya ci kwallaye 21 a wasanni 23 da ya buga wa Napoli a kakar wasa ta bana.