Jamiāin yada labarai na Super Eagles, Babafemi Raji, ya karyata rahotannin da ke yawo cewa, Victor Osimhen ya fice daga wasan sada zumuncin da kungiyar da za ta yi da Portugal da gangan.
Osimhen dai ya fuskanci suka sosai, bayan ya fice daga wasan sada zumunci sakamakon raunin da ya samu.
Har ila yau dan wasan bai buga wasan sada zumuncin da Super Eagles ta yi da Desert Foxes ta Algeria a watan jiya ba.
Dan wasan mai shekaru 23, ya shafe mintuna 90 yana wasa a kungiyarsa ta Seria A, Napoli ta doke Udinese da ci 3-2 a karshen makon da ya gabata.
Raji ya bayyana cewa Napoli ta aika da hoton MRI na raunin da ya samu ga tawagar likitocin Super Eagles.
āOsimhen ya ji rauni. Haka ne, ya buga wasan karshe na kungiyarsa, amma likitocin Napoli sun aika MRI (scans) zuwa kungiyar.
“Yanzu zai yi hutu na tsawon kwanaki 15.”
Dan wasan gaba na Cremonese, an kira Cyriel Dessers a matsayin wanda zai maye gurbin Osimhen.