fidelitybank

Osibanjo ya yabawa hukumar jarabawar WAEC

Date:

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Litinin a Abuja, ya yaba wa hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma WAEC.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar hukumar jarabawar da ke garin, domin halartar taron majalisar na shekara karo na 70 a fadar shugaban kasa.

Babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Laolu Akande, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Litinin mai taken ‘Dole ne hukumomin gwamnati su rika girmama ‘yan kasa, su rika daukar nauyinsu.

“Don haka ina taya ku, ’yan Najeriya da Hukumar WAEC murna, ba wai don an ba ku dama ta musamman na gudanar da bikin cikar shekaru 70 ba, har ma saboda a fili yake mu ne muka fi kowa bayar da gudumuwa da cin gajiyar wannan shiri tsawon shekaru 70.

A nata jawabin, shugabar a Najeriya ta WAEC, wadda kuma ita ce Daraktar Ilimin Basic & Sakandare na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Binta Abdulkadir, ta godewa gwamnatin tarayyar Najeriya bisa damar da ta samu na karbar bakuncin taron majalisar shekara karo na 70. da kuma goyon bayan da Majalisar ta yi a tsawon shekaru.

latest nigeria newstoday

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp