fidelitybank

Osibanjo da Tinubu su barwa ƙabilar Inyamurai takarar shugaban ƙasa – Ƙungiyar Afenifere

Date:

Shugaban majalisar tuntuɓa ta ƙabilar Yarbawa, Afenifere, Cif Ayo Adebanjo ya nemi masu neman takarar shugabancin Najeriya daga yankin Kudu maso Yamma da su haƙura kawai.

Shugaban ƙungiyar al’ummar Yarbawa ya ce, ya kamata ‘yan takarar yankin na su kamar Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo su bar wa ‘yan ƙabilar Igbo, domin samar da shugaban ƙasa na gaba a 2023.

Jagoran ya bayyana hakan ne cikin wata hira da jaridar Punch ranar Talata, ya na mai cewa “rashin adalci ne ɗan Kudu maso Yamma ya zama shugaban ƙasa, bayan Olusegun Obasanjo ya mulki Najeriya shekara takwas, sannan kuma Yemi Osinbajo zai shekara takwas a muƙamin mataimakin shugaban ƙasa”.

Sai dai kuma dattijon mai shekara 94, ya ce, “dole ne a kyautata ƙasar kafin Najeriya ta samu sabon shugaba”.

“A yanzu akwai ƙasar ma da suke so su shugabanta? Wajibi ne a samar da dunƙulalliyar ƙasa kafin ka yi maganar zaɓe,” in ji shi.

the sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kotu ta yanke wa Matashin da ya kashe Budurwarsa hukuncin kisa

Kotun babban birnin jihar Nasarawa ta yanke wa wannan...

PDP ta yi watsi da matakin shugaban jam’iyyar da ya dauka

Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, ya yi watsi da...

Tinubu zai sanya hannu kan sabbin dokokin haraji

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai sanya hannu kan...

‘Yan Bindiga sun kashe Sojoji a Neja

Rundunar Sojin Kasa, ta tabbatar da mutuwar wasu daga...

Kungiyoyi 110 suna bukatar mu yi musu rijista – INEC

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta tabbatar da samun buƙatu...

Majalisar dokoki na son Iran ta yanke hulɗa da hukumar sanya ido kan makamashin nukiliya

Majalisar dokokin Iran ta kaɗa ƙuri’a domin yanke hulɗa...

Ƴan sanda sun kama mutum 26 da ake zargi da hannu a kashe-kashen Benue

Sufeto Janar na ‘ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana...

Ba dan mun yi wa Iran barna ba da har yanzu ba ta nemi sulhu ba – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake jaddada cewa harin...

Iran ta zartar da hukuncin kisa kan masu leken asiri

Kamfanin dillancin labarai na sashen shari'a a Iran ya...

Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...
X whatsapp