Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, da gwamna Dave Umahi na Ebonyi sun tattauna da wakilan jam’iyyar APC a Imo.
Mutanen uku sun tuntubi wakilan ne a wata ganawa daban-daban a Owerri, babban birnin Imo, a ranar Talata, gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka shirya gudanarwa a ranar 29 ga watan Mayu.
Shima da yake jawabi a lokacin da yake tuntubar sa, Gwamna Umahi ya yi alkawarin baiwa Najeriya alfahari idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023.