Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, shugaban jamâiyyar APC na kasa, Sanata Abudullahi Adamu da gwamnoni biyar na kungiyar gwamnonin ci gaba sun yi ganawar sirri a yammacin ranar Alhamis.
Taron wanda ya gudana a gidan Mataimakin dake Aso Rock, na zuwa ne kwanaki biyar kadan kafin gudanar da zaben fidda gwanin da ake jira a ranakun 6 da 8 ga watan Yuni.
Ba a san manufar taron ba, domin kawo yanzu dai ba a rasa nasaba da yunkurin neman amincewar juna kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukata.
Idan dai za a iya tunawa, kafin ziyarar tasa a birnin Madrid na kasar Spain, shugaban kasar ya gana da gwamnoni 22 na jamâiyya mai mulki, inda ya jaddada bukatar su ba shi goyon baya wajen zaben dan takarar jamâiyyar.