Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, a yau Laraba, ya dawo Najeriya, bayan hutun makwanni biyu da ya yi a kasar Birtaniya da kuma Amurka.
Gwamnan ya samu tarba ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe tare da manyan jami’an jam’iyyar da na gwamnatin jihar da ke Abuja da safiyar Laraba.
Idan dai za a iya tunawa Ortom a ziyarar da ya kai kasar Amurka ya yi kira ga gwamnatin Amurka da sauran al’ummomin duniya da su kama shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa da hannu wajen kashe-kashen da ake yi a Najeriya. In ji Daily Post.
Gwamnan wanda ya yi wannan kiran a ma’aikatar harkokin wajen Amurka da ke Washington DC a lokacin da yake zantawa da jami’anta, ya kuma zargi Fulani makiyaya da amfani da su a matsayin makami wajen kawar da manoma daga yankunan kakanninsu.
Ortom ya kuma shaida wa gwamnatin Amurka cewa “an yi wa noma a Najeriya kawanya kuma ana lalata shi; noma na mutuwa sannu a hankali kuma ana fuskantar barazanar samar da abinci”.