fidelitybank

Orji Kalu ya yi Allah wadarai a kan harin da aka yi wa shugaban Inyamurai

Date:

Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Orji Kalu, ya yi Allah-wadai da harin da aka kai gidan shugaban kungiyar ƙabilar Inyamurai Ohaneze Ndigbo, Farfesa George Obiozor a Awo- Omanma.

Wasu ‘yan bindiga ne suka kona gidan dan siyasar da sanyin safiyar Asabar.
Kalu a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja, ya bayyana wannan aika-aika a matsayin mugun abu, zalunci da mugunta.

Ya kuma yi kira ga hukumomin da suka dace da su binciki mumunan lamarin da nufin gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Tsohon Gwamnan na Abia ya jaddada cewa, dan jihar mutum ne mai son zaman lafiya a Najeriya, wanda ya ci gaba da dauwama da kyawawan halayensa duba da irin halayensa da jajircewarsa na gina kasa.

Kalu ya zargi maharan kan abin da ya bayyana a matsayin rashin wayewa, inda ya kara da cewa tashe-tashen hankula da munanan dabi’u na da illa ga ci gaba da ci gaban al’umma.

Kalu ya yi kira ga Ndigbo da ‘yan Najeriya baki daya da su rungumi zaman lafiya da hadin kai domin gina kasa.

legit com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp