Tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Kalu, ya caccaki shugaban kungiyar Pan Niger Delta Forum (PANDEF), Cheif Edwin Clark, inda ya kira dattijon a matsayin mai cin amanar yankin Kudu maso Gabas a yunkurin da yankin ke yi na samar da shugaban kasa a 2023.
Martanin Kalu ya zo ne a daidai lokacin da Clark ya yi kakkausar suka kan ficewar Shugaban Majalisar Dattawa daga takarar Shugaban kasa a 2023 tare da bayyana goyon bayansa ga Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Larabar da ta gabata, tsohon kwamishinan yada labaran gwamnatin tarayya ya caccaki Kalu kan cin amanar yankin Kudu maso Gabas inda ya yi watsi da takararsa ya goyi bayan dan takarar Arewa.