Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da sabon shirin tsaro mai suna Operation Kukan Kura, domin karfafa aikin ‘yan sanda na al’umma da kuma yaki da laifuka.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce shirin zai karfafa hadin kai da jama’a, inda mazauna za su taka rawa a matsayin “idanu da kunnuwan ‘Yan Sanda”.
Ya ce irin wannan tsari ya taimaka a baya wajen shawo kan matsalar Fadan Daba a Kano.
Bakori ya bayyana cewa a watan Agusta kadai, an kama mutum 107 da ake zargi da laifuka daban-daban ciki har da fashi da makami, garkuwa da mutane, safarar miyagun kwayoyi da sata, tare da kwato bindigar AK-47, bindigogi 7, harsasai, motoci, babura, shanu da miyagun kwayoyi.
Ya kara da cewa a shekarar 2025 kadai, an kwato daruruwan makamai masu hadari da miyagun kwayoyi, inda ya yaba wa jami’an ‘yan sanda da amfani da fasahar zamani wajen inganta aiki.
Kwamishinan ya yi alkawarin ci gaba da kirkiro sabbin dabaru don tabbatar da tsaro, tare da gode wa jama’a da kafafen yada labarai kan hadin kai.
“Bayar da bayanai daga jama’a ya karfafa ikonmu na tabbatar da tsaro a jihar,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga mazauna Kano da su ci gaba da kai rahoton duk wani abu da ke da alamar laifi ko hatsari ga hukumar.