fidelitybank

Olympics: An soke jigilar wasu jiragen ƙasa a Faransa bayan hari kan layin dogon

Date:

An soke uku daga cikin layin dogo 10 mafi gudu a Faransa ranar Asabar, bayan da wasu mahara suka ƙaddamar da hari kan layin dogon ƙasar ranar Juma’a gabanin bikin buɗe gasar Olympics a birnin Paris.

Firaministan ƙasar,Gabriel Attal ya ce jami’an tsaro na ci gaba farautar maharan layin dogon da ya kira da ”masu zagon ƙasa”, da ke neman gurgunta sufurin jiragen ƙasa a Faransa, a daidai lokacin da aka fi buƙatar amfani da jiragen.

Hukumar sufurrin jiragen ƙasa ta ƙasar, ta ce za a jinkirta amfani da wasu layin dogon da ke kai wa da komowa zuwa birnin Paris a ranar Asabar da kusan sa’a biyu, yayin da za a soke kashi ɗaya cikin huɗu na jiragen da ke jigila tsakanin ƙasashen nahiyar Turai.

Ministan sufurin ƙasar, ya ce zuwa ranar Litinin komai zai daidaita duka titinan jiragen za su koma aiki.

A ranar Juma’a ne dai wasu mutane da ba a san kosu wane ne ba suka kai hari kan wasu titunan layin dogon, inda suka cinna wuta tare da yanke wasu muhimman wayoyin layin dogo, gabanin bikin buɗe gasar Olympics a birnin Paris.

Kawo yanzu babu wata ƙungiya ko wasu gungu da suka ɗauki alhakin harin, sai dai hukumomi na ci gaba da bincike.

Wata majiya mai alaƙa da binciken da ta shaida wa kamfanin dillancin labaran ƙasar, AFP cewa maharan sun ”shirya” sosai kafin su ƙaddamar da harin. In ji BBC.

vgn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp