Dan wasan baya na Najeriya, Ola Aina zai koma atisaye nan da ‘yan kwanaki masu zuwa bayan ya yi jinya.
Aina ya kasa buga wa Torino wasa tun bayan raunin da ya samu a wasan da kungiyar ta doke Udinese da ci 2-1 a ranar 23 ga Oktoba.
Dan wasan mai shekaru 26 bai buga wasanni hudu na karshe na kungiyar Ivan Juric ba sakamakon koma baya.
A cewar Torino Granata, Aina ya rage ‘yan kwanaki da shiga horon tawagar farko na Torino.
Ana sa ran ƙwararren mai tsaron baya zai haɗu da takwarorinsa na Torino a Philadelphia, Amurka, ranar Litinin mai zuwa.
‘Yan wasan Torino, wadanda ba su da hannu a gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2022, za su je Amurka don yawon shakatawa.
Aina ya buga wasanni 10 a kungiyar Torino a kakar wasa ta bana tare da zura kwallo a raga.