Tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya biya tarar naira miliyan 13 don gujewa zaman gidan yari.
A ranar Litinin ne wata Babbar Kotu a birnin tarayyar Najeriya Abuja ta yanke wa Doyin Okupe hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari bayan gabatar da ƙwararan hujjoji da ke nuna cewa Mista Okupe ya karɓi kuɗaɗe lakadan na biyan wasu ayyuka a yayin da yake gudanar da aikinsa, kuma bai kai kudin asusun da ya kamata ba.
Tun a shekarar 2019 ne EFCC ta gurfanar da Mista Okupe a gaban kotu kan zargin almundahanar.
An zargi Okupe da karɓar kuɗaɗe daga ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara an sha’anin tsaro, waɗanda ya gaza yin bayani kansu.
An yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyun ne bayan kama shi da laifi 25 daga cikin tuhuma 59 da ake masa.
Tuhume-tuhumen dai sun ta’allaƙa ne a kan karɓar makuɗan kuɗaɗe kama daga naira miliyan 10, a wasu al’amura daban-daban daga shekarar 2012 zuwa 2015.
Mr Okupe, ya biya tarar ce, bisa zaɓin biyan tarar naira 500,000 kan kowace tuhuma da ake masa da kotu ta bashi.
Tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban na Najeriya, ya biya tarar ce tun kafin wa’adin da aka gindaya masa.