Gwamnan jihar Delta kuma mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Ifeanyi Okowa, ya gana da takwaransa na jihar Benue, Samuel Ortom.
‘ya’yan jam’iyyar PDP guda biyun, sun gana a ranar Alhamis a Abuja a wajen bikin rantsar da Most Reverend Daniel Okoh a matsayin sabon shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).
Wannan lamari dai na zuwa ne watanni, bayan Ortom a wata hira da yayi da gidan Talabijin na Channels TV ya yi Allah wadai da fitowar Okowa a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.
Ortom ya zargi Atiku da yin watsi da lauyoyin kwamitin da aka kafa domin zabar dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.


