Ahmed Usman Ododo, tsohon mai binciken kananan hukumomi a jihar Kogi, ya zama dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan jihar Kogi.
Ododo, wanda ya samu kuri’u 78,704, ya lashe zaben fidda gwanin da aka gudanar a ranar Juma’a, da tazara mai yawa inda ya doke wasu ‘yan takara shida a zaben gwamnan.
Karanta Wannan: An fara kammala zaɓe a Kano
Ya doke wanda ya zo na biyu, Barr. Mohammed Ozigi Salami, wanda ya samu kuri’u 1,506, yayin da Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Smart Adeyemi, ya samu mafi karancin kuri’u – 311.
Hon. Patrick Obahiagbon, sakataren kwamitin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC reshen jihar Kogi, a madadin shugaban kwamitin, gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ne ya bayyana sakamakon zaben.
Obahiagbon ya ayyana Ododo a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamna.


