A yayin da aka tabbatar da kammala kidaya kusan rabin kuri’un da aka jefa a zaɓen shugabancin ƙasar Kenya, manyan ‘yan takarar biyu na tafiya kai da kai.
Mataimakin shugaban kasa, William Ruto ya ɗan bai wa tsohon firaminista Raila Odinga tazara kada – kashi 51 da 48 cikin 100.
Shugaban hukumar zaɓe na kasar ya ce tabbas ana samun jinkiri wajen kidaya in ji BBC. kuri’un.
Sau da dama ana dakatar da kidaya kuri’a biyo bayan korafe-korafe daga magoya bayan jam’iyyu.
A ranar Asabar, magoya bayan Mista Odinga sun farwa wani yankin da jami’an zaɓe ke aiki, tare da zarginsu da coge.
Yayinda su kuma magoya bayan Mista Ruto ke zargin cewa ana katsalanda a harkokin kidaya kuri’a.
An dai tsaurara tsaro na baza jami’an kwantar da tarzoma a kowanne bangare na kasar.
Kawo yanzu dai an tabbatar da kammala kidaya kuri’un mazabu 141 cikin 292.
Kuma an bai wa kafofin yada labarai bayanai kan sakamakon wucin-gadi na wadannan mazabu, wanda ke nuna ‘yan takarar biyu na tafiya kai da kai.
Kusan mutum miliyan 14 ne suka fita zabe.


