Kyaftin din Arsenal Martin Odegaard ya rattaɓa hannu kan sabuwar kwantiragin shekara biyar.
Dan wasan tsakiya na Norway, mai shekara 24, ya ci ƙwallaye 27 kuma ya taimaka aka ci 15 a wasanni 112 da ya buga wa Gunners.
Odegaard ya koma kulob din ne daga Real Madrid na zaman dindindin a watan Agustan 2021 kan farashin fam miliyan 30 bayan ya yi zaman aron na kaka daya.
Ya buga wasanni 38 da Arsenal ta buga a gasar Premier a bara yayin da kungiyar Mikel Arteta ta ƙare a matsayi na biyu a bayan Manchester City kuma ta kawo ƙarshen rashin halartar gasar cin kofin Zakarun Turai na tsawon kaka shida.
Odegaard, wanda har ila yau shi ne kyaftin ɗin tawagar Norway inda ya buga wasanni 53, ya ƙulla yarjejeniya da Arsenal har zuwa ƙarshen kakar wasa ta 2027-28.
Ya ci wa Arsenal ƙwallaye uku a wasanni bakwai a kakar wasa ta bana – ciki har da wanda ya ci ranar Laraba yayin da kulob din ya buga wasan farko na gasar cin kofin zakarun Turai na kakar wasan bana inda Arsenal ta doke PSV Eindhoven da ci 4-0.
Odegaard na daya daga cikin Manyan ‘yan wasan Kulob din da suka tsawaita kwantiraginsu bayan Bukayo Saka ya amince da sabuwar yarjejeniya na ci gaba da zama a Arsenal har zuwa shekarar 2027 a watan Mayu, sai dan wasan baya William Saliba, da mai tsaron gida Aaron Ramsdale da kuma dan wasan tsakiya Reiss Nelson su ma za sun ƙulla yarjejeniyar tsawaita kwantiragin dogon zango a bana


