Ɗaya daga cikin ‘yan takarar da shugaban kasa a zaɓen 2023, Peter Obi, ya caccaki gwamnatin Tinubu da majalisar wakilai ta ƙasar dangane da batun da suka fara yi na sayan ƙarin jirage ga shugaban ƙasa.
Mista Obi ya bayyana al’amarin da abin da ba zai yiwu ba “sannan yana nuna rashin tausayi ga wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki ba”.
Peter Obi ya yi sukar ne a shafinsa na X ranar Litinin, inda ya ce “A daidai lokacin da sunan ƙasarmu ya ɓaci a jaridun duniya sakamakon halin matsin tattalin arziƙin da take fuskanta saboda hauhawar farashi da karyewar darajar naira da baƙin talauci, amma wai gwamnati na tunanin ƙara wa tawagar shugaban ƙasa jirage”.
Ɗan takarar jam’iyyar ta LP, ya ƙara da cewa “a bayyane take cewa jiragen shugaban ƙasa sun kai shekara 12 kuma an saye su ne tun lokacin ‘yan Najeriya na iya biyawa kansu buƙatu. A yanzu kuma da kasar tamu ke fuskantar manyan matsaloli da suka haɗa da bashi da rashi da ‘yan kasar ke fama da shi, maimakon ƙara abubuwan jin daɗi ya kamata mu yi koƙarin yaye musu wahalhalun da suke ciki”.
Daga karshe mista Obi ya ce maimakon saye-sayen da ba za su ƙara wa ‘yan najeriya komai ba “ dole ne mu mayar da hankali a kan ilimi da kiwon lafiya da yaye wa ‘yan Najeriya talauci…”