Jam’iyyar Labour, LP, ta nada tsohon mai baiwa shugaban kasa Olusegun Obasanjo shawara kan harkokin siyasa, Akin Osuntokun a matsayin sabon Darakta Janar na yakin neman zaben shugaban kasa.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Julius Abure, ya tabbatar da hakan a Abuja, ranar Talata.
A cewar Abure, an cimma matsayar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a fadin kasar.
Yanzu Osuntokun zai maye gurbin Doyin Okupe wanda ya yi murabus daga mukamin a makon jiya.
Okupe ya sauka daga mukamin ne biyo bayan hukuncin wata babbar kotun tarayya wadda ta same shi da laifin karkatar da kudade.
Kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari amma da zabin biyan tarar N500,000 akan kowanne tuhume-tuhumen da ya kai Naira miliyan 13.
Okupe ya zabi ya biya tarar bayan yanke hukuncin.