Bayan harin bazata da sojoji suka kai a ƙauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da isassun kudade ga sojoji da sauran hukumomin tsaro domin inganta ayyukansu.
Obi ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ziyarci waɗanda abin ya shafa a asibitin koyarwa na Barau Dikko da ke babban birnin jihar a ranar Talata.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Obi na koka wa da cewa kawo yanzu ƙasar nan ta samu tashin bama-bamai 16 da sojoji suka yi bisa kuskure da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 500, ba tare da wani abu da Gwamnatin Tarayya ta yi ba wajen ganin an daƙile aukuwar irin wannan bala’i.
Sai dai Obi ya jaddada buƙatar gwamnati ta tallafa wa sojoji don ganin ba a sake samun tashin bama-bamai na bazata ba.
Obi ya lura cewa isassun kudade ga sojoji shine mabuɗin wajen tinkarar matsalolin tsaro da ke addabar al’umma a wannan zamani.
Ya goyi bayan kiraye-kirayen a binciki harin da sojoji suka kai ta sama, kamar dai yadda ya bayar da shawarar kafa wata gidauniya da za ta tallafawa waɗanda harin Tudun Biri ya rutsa da su, musamman wadanda lamarin mai da su marayu.