fidelitybank

Obi ya jagoranci tawagar Lauyoyinsa zuwa kotu

Date:

Ɗantakarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP) Peter Obi, ya ce, shi da kansa zai jagoranci lauyoyin jam’iyyarsu yau Laraba, zuwa kotu saboda hukumar zaɓe, INEC, ta ƙi ba su kayan da aka yi amfani da su a zaɓen da aka yi su duba, kamar yadda kotu ta umarta.

A saƙon da ya sa a shafinsa na Twitter Mista Obi ya ce ba zai samu damar zuwa yaƙin neman zaɓe na gwamnoni da ƴan majalisar dokoki na jihohin da aka tsara zai yi ba saboda zuwa kotun.

Karanata Wannan: Lauyoyi 19 na Atiku da na Tinubu 12 suna fafatawa a kan zabe

Ya ce a da an tsara zai je jihohin da suka haɗa da Nasarawa da Lagos da Enugu da Abia da Delta da Edo da Rivers da Plateau da Borno, to amma ya fasa hakan domin ya jagoranci tawagar lauyoyin da kansa zuwa kotun a Abuja.

Mista Obi, wanda ya ce za su ci gaba da wannan fafutuka ta fuskar shari’a domin ƙwato nasarar da ya ce an sace musu, ya buƙaci magoya bayansa da za su je kotun da kada su mayar da harabar wajen zanga-zangar siyasa.

Sannan ya buƙaci magoya bayan nasa da ake musu laƙabi da Obidients da su mara wa ‘yan takararsu a jihohin da za a yi zaɓen gwamnonin da ‘yan majalisar jiha baya, su kuma kasance masu bin doka.

dailypostnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp