Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, LP, Peter Obi ya doke sauran ‘yan takarar shugaban kasa a jihar Cross River da tazarar kuri’u 179,917.
Jami’in tattara bayanai na jihar, Farfesa Akpofure Rim-Rukeh ya bayyana sakamakon zaben da safiyar Talata.
APC ta samu kuri’u 130,520, PDP ta samu kuri’u 95,425, NNPP ta samu kuri’u 1,644.
Karanta Wannan: Da Dumi-Dumi: Tinubu ne a kan gaba a sakamakon zaben 2023
Da yake tsokaci kan yanayin da jihar ke da shi kan jinkirin, kwamishinan zabe na jihar, Farfesa Gabriel Yomere ya nemi afuwar sakamakon kammala tattara sakamakon zaben.