Tsohon shugaban tsagerun Neja Delta, Mujahid Asari Dokubo, ya yi watsi da ikirarin cewa, zababben shugaban kasa, Bola Tinubu bai tafka magudi ba a zaben shugaban kasa na 2023.
Asari Dokubo ya ce sabanin ikirari, jamâiyyar Labour Party, LP, dan takarar shugaban kasa Peter Obi ne suka tafka magudi a zaben shugaban kasa da aka kammala ba Tinubu ba.
Obi da Atiku Abubakar na jamâiyyar PDP, sun fafata ne a zaben shugaban kasa na karshe da ya samar da Tinubu.
Dukkan mutanen biyu dai na fafatawa da sakamakon zaben shugaban kasar ne a gaban kotu, inda suka jaddada cewa sun lashe zaben.
Da yake magana a shafin Facebook Live a ranar Litinin, dan fafutukar Neja Delta ya jaddada cewa Obi ba shi da hurumin koka game da sakamakon zaben.
âZaben da aka yi a duk fadin kasar nan ya nuna cewa wanda ya yi magudin zaben shi ne Peter Obi. Sakamakon a bayyane yake.
âIdan suka kalli zaben da kyau, ba zai iya samun kuriâu miliyan biyu ba. A zabe na gaskiya ko a Anambra Obi ba zai yi nasara ba,â in ji Dokubo.