Wani dan fafutuka, Deji Adeyanju ya caccaki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi kan dabarun yakin neman zabensa.
Adeyanju ya ce Obi yana zuwa coci-coci maimakon ya ziyarci kananan hukumomi 774 domin gina siyasar sa.
Ya bayyana hanyar Obi a matsayin wani yunkuri na rashin hankali, yana mai cewa tsohon gwamnan jihar Anambra yana sa ran majami’u su zama tsarinsa.
“Obi ya zagaya coci-coci yana tsammanin za su yi masa tsarin siyasa a watan Fabrairu maimakon kawai ya zagaya kananan hukumomi 774 don gina kamar yadda yawancin jam’iyyun siyasa ke yi, shi ne mataki mafi rashin hankali da na taba gani.
“Ya kasance a coci a Benue jiya kuma. Kusan watanni 3 bayan kammala zaben fidda gwani na jam’iyyar, har yanzu ba su fara gina jam’iyyar a ƙananan hukumomi a ko’ina a Najeriya ba. Suna sha’awar hayaniyar shafukan sada zumunta ne kawai da kuma Maris miliyan 1 wanda bai kai 2k ba,” in ji Adeyanju a cikin wani sakon ranar Litinin.


