Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jamiyyar LP, Peter Obi ba zai taɓa zama shugaban Najeriya ba.
A ƙarshen mako ne Peter Obi ya bayayna aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaɓen 2027 ƙarƙashin sabuwar haɗakar ADC.
To sai dai yayın da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamar da wasu ayyuka a Abuja, tsohon gwamnan na jihar Rivers, ya ce burin na Mista Obi ba zai taɓa cika ba.
E “Ana cewa Peter Obi zai zama shugaban ƙasa, amma wacce ƙasa? Ku ba ku san wasu mutanen ba, kawai suna faɗin duk abin da ya zo bakunansu ne”, in ji Wike.
“Ta yaya ƴan Najeriya za su amince da kai, a shekarar 1999 kana wata jamiyya, a 2006 ka shiga wata, haka ma a 2014 kana wata daban, sannan a 2019 ka sake komawa wata, yanzu a 2025 ka ce ka shiga wata don ceto ƙasa, wa za ka ceto?, inj Ministan na Abuja