Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya ce ɗaya daga cikin jagororin sabuwar haɗakar ADC, Peter Obi ba zai iya cin yankin arewacin Najeriya a zaɓen 2027, sakamakon yadda Shugaba Tinubu ya kafu a yankin.
Yayin wata hira da gidan talbijin na Channels, Keyamo ya ce Shugaba Tinubu da jam’iyyarsa ta APC, sun samu kafuwa da tsari a yankin arewacin Najeriya.
Ministan jiragen saman ya kuma ce da wahala haɗakar ADC ta iya yin wani tasiri a fagen siyasar ƙasar.
”Babu inda za su je, indai don batun samun magoya baya ne”, in ji Keyamo.
“Wannan haɗakar da suke kira ADC, abin da take yi shi ne ƙoƙarin haɗa Atiku da Obi a 2027, domin zartar adadin ƙuri’a miliyan takwas da muka samu a 2023”, in ji shi.
A zaɓen 2023 da Tinubu ya yi nasara ne da ƙuri’a sama da miliyan takwas, yayin da Atiku da ya zo na biyu ya samu ƙuri’a kusan miliyan bakwai, sai Peter Obi da ya zo na uku ya samu ƙuri’a sama da miliyan shida.