fidelitybank

Obasanjo ya tuka babur mai kafa uku dauke da fasinjoji

Date:

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya tuka babur mai kafa uku a ranar Asabar.

Obj, kamar yadda aka fi sani da suna, ya bi ta wasu hanyoyi a Abeokuta, babban birnin Ogun, don daukar fasinjoji.

Lamarin ya dauki hankulan mutane da dama wadanda suka yi wa tsohon Shugaban kasar murna tare da daukar hotuna.

Dattijon wanda ya yi wa ’yan kasa kyauta, ya zarce ta Moshood Abiola, NNPC Mega Station, Kasuwar Kuto, da dai sauransu.

Aikin wani bangare ne na shirin Keke na OBJ @ 85 na Cibiyar Bunkasa Matasa na Laburaren Shugaban Kasa na Olusegun Obasanjo (OOPL).

A cikin jawabinsa, Obasanjo ya yi kira ga matasa da kada su bar Najeriya ga masu tada zaune tsaye.

Tsohon shugaban ya ce, duk da kalubalen da ake fuskanta, ya kamata su yi kokarin amfani da damar da ake da su don yin tasiri.

“Abubuwa ba abin da ya kamata su kasance ba amma dole ne matasa a daidaiku da kuma a dunkule su ba da gudummawa don ganin abubuwa su kasance kamar yadda ya kamata.

“Idan kun bar abubuwa ga masu yi muku almundahana da cewa ku ne shugabannin gobe, ba za ku taba samun haka gobe ba.

“Allah ya baka ikon zama abin da yake so ka zama. Idan kuka yanke shawara, Allah zai taimake ku ya samar da mutanen da za su taimake ku,” ya kara da cewa.

nigerianews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp