Gwamnan Edo Godwin Obaseki, ya kafa kwamitin zaman lafiya a ranar Lahadi a Benin, domin warware rikicin da ya dabaibaye jamâiyyar PDP reshen jihar.
Kwamitin yana kunshe da tsohon Gwamna Lucky Igbinedion a matsayin shugaban kwamitin.
Obaseki ya bayyana hakan ne a wajen kaddamarwar, inda ya ce, sun dauki matakin ne domin dakile yuwuwar shan kaye a jamâiyyar PDP a jihar a zaben 2023 mai zuwa.
Mambobin jam’iyyar PDP 135 da suka halarci taron sun fito ne daga kwamitin zartarwa na kasa, kwamitin zartarwa na jiha da na shiyya.
- Gwamnan ya ce, an kira taron ne domin warware duk wata rigima a cikin jamâiyyar domin samun nasara a zaben 2023 mai zuwa.
Obaseki ya ce taron ya zama dole ne biyo bayan kayen da jamâiyyar APC da Social Democratic Party (SDP) suka yi wa jamâiyyar PDP a zaben gwamnan Ekiti da aka yi ranar Asabar.
Ya ce, don gudun kada a sake samun nasara a zaben Ekiti a zaben shugaban kasa a 2023, PDP a Edo na bukatar hada kai tare da warware sabanin da ke tsakanin âyaâyan kungiyar tare da hada kowa da kowa domin samun nasara.