Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya ayyana zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na 2023 a jihar Ogun cikin kwanciyar hankali da inganci.
Obasanjo ya bayyana ra’ayinsa ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida bayan kada kuri’arsa a Abeokuta.
Tsohon shugaban kasar wanda ya kada kuri’a da misalin karfe 10:32 na safe a Unguwa 11, rumfar zabe ta 22 da ke Olushomi Compound, yankin Sokori a Abeokuta – Arewa, ya nuna jin dadinsa kan yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana.
Karanta Wannan: Osinbajo da Matarsa sun kaɗa kuri’arsu a Ogun
Ya ce, “Ina ganin muna samun nasara a zabe a kasarmu.
“Mutane na iya ganin abubuwan da ke karfafa gwiwa da kuma ba da bege na gaba dangane da zaben saboda an samu ci gaba.
“Na shigo aka duba ni. Aka ce in cire gilashina aka sanya na’urar a gaban fuskata kuma hotona ya bayyana.
“Wannan sabon abu ne kuma idan hakan zai faru a duk fadin kasar, ina ganin muna samun ci gaba.
“Ya kamata mutum ya karfafa da kuma goyon bayan duk wani abu da zai taimaka wajen sahihanci, gaskiya da kuma bayyana gaskiya a tsarin zabe saboda ingantaccen zabe shi ne farkon gudanar da kyakkyawan shugabanci na kowace kasa.”