Dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar Labour Party (LP), Peter Obi, a ranar Laraba ya yi magana kan rahoton da ke ikirarin cewa, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo na sayar da takararsa ga Arewacin Najeriya.
Shi ma tsohon gwamnan jihar Anambra a martanin sa ya ce, babu laifi Obasanjo ya goyi bayan aniyar sa ta shugaban kasa.
Obi ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a safiyar Laraba.
Dan takarar shugaban kasar ya ce, âMe ke damun Obasanjo ya sayar da takarata. Su (Arewa) ma suna sayar da takarata. Dan takarar shugaban kasa na NNPP da mai magana da yawunsa, babban yayana Buba Galadima duk sun fadi haka.
âIna cewa muna da matsalar tattalin arziki. Ba ma buĈatar wani ya kasance a kaina lokacin da zan iya magance matsalar, kuma abin da nake bayarwa ke nan. Ina neman zama shugaban Najeriya. Ina iya fitowa daga wani sashe na kasar nan, amma ina so in warware matsalar Najeriya.â
Wannan na zuwa ne bayan shugaban kungiyar ta tattaunawa, Mahdi Shehu ya ce Obasanjo na tallata Obi, a Arewa.
Shehu ya ci gaba da cewa Obasanjo yana ziyartar manyan mutane a Arewa domin sayar da Peter Obi.