Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma daya daga cikin iyayen da suka kafa Jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya ce, tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba komai ba ne in ba PDP ba.
Lamido ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga amincewa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party LP, Peter Obi da tsohon shugaban kasar ya yi.
Sai dai Lamido ya ce, abin kunya ne Obasanjo ya amince da wani daga wata jam’iyyar ba dan takarar jam’iyyar da ya sa ya zama kamar shi a yau ba.
“Abin da ya ke fada shi ne saboda shi tsohon shugaban ƙasa ne a karkashin jam’iyyar (PDP) ya kirkiro shi, ya karrama shi, ya kuma ba shi martaba a duniya.”
“Shekaru ashirin da biyar ba zai fadi abin da ya ke fada ba, don haka abin kunya ne a ce sabuwar PDP ta ruguza jam’iyyar.”
“Obasanjo ne shugabana da na sani, amma mutum ne kuma zai yi kuskure, don haka ya yi babban kuskure wajen amincewa da wata jam’iyya a wajen jam’iyyarsa.”
“Akan batun karba-karba, mutane ba su da gaskiya, idan ana maganar adalci da gaskiya.
Guba ce zalla a kan dan takarar Obasanjo – Tinubu
“Lokacin da ya ke kan karagar mulki, ya yi kokari karo na uku. Shin hakan gaskiya ne, wannan adalci ne? Ba haka ba. Ina girmama shi amma dole ne mu tsaya kan al’adarmu, tarihin jam’iyyarmu, falsafar mu, da kuma PDP sun sanya Najeriya ta kasance a yau.”