Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da abokin takararsa, Yusuf Datti Baba-Ahmed, a ranar Lahadi, sun ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun.
Mutanen biyu sun gana da Obasanjo tare da Shugaban Jam’iyyar Labour Party (LP) na kasa, Julius Abure, da Babban Fasto, Cocin Trinity House, Ituah Ighodalo.
Baba-Ahmed ya bayyana hakan sannan kuma ya raba hotunan ganawar da Obasanjo a shafin sa na Twitter.
Sai dai ya yi shiru kan batutuwan da aka tattauna a taron.
“A safiyar yau (Lahadi), ni da H. E. #PeterObi tare da wasu jiga-jigan # NgLabour mun tuntubi tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo,” in ji shi.