Mukaddashin Kwamandan Janar , Fasiu Adeyinka, Ko’odinetan shiyyar tsaro na NSCDC na Osun, Ondo da Ekiti, ya yabawa masu zabe, bisa yadda suka yi zabe cikin lumana a zaben gwamnan Osun da ke gudana.
Adeyinka ya yi wannan yabon ne a lokacin da ya ziyarci makarantar firamare ta St. Gabriel Yemoo, Moore, Ward 3 da 4, Rukunin zabe 003 da 004, a ranar Asabar, a Ile-Ife.
Ya ce, masu kada kuri’a sun kasance cikin nutsuwa, sanyi da sauki a duk ranar da aka ziyarta ba tare da wata matsala ba.
A cewarsa, masu kada kuri’a suna da manufarsu da kyau ba tare da tunanin komai ba.