Hukumar tsaro ta NSCDC, ta tura jami’ai 9,747, domin gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti da za a yi ranar Asabar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar NSCDC Olusola Odumosu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.
Sanarwar ta ce, Kwamandan NSCDC, Janar Ahmed Audi, wanda ya amince da aikewa da jami’an, ya umarci dukkan ma’aikatan da ke da ruwa da tsaki a harkokin zabe da su kasance masu kwarewa wajen gudanar da ayyukansu.
Audi ya shawarci jami’an da su yi aikinsu daidai da ka’idar tsarin aiki na rundunar, wanda ke zama jagora a ayyukan su.