Rundunar tsaro ta Civil Defence reshen jihar Delta, a karshen mako ta ce, ta kama sama da mutane 42 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da fasa bututun mai, satar danyen mai, garkuwa da mutane da lalata da yara da safarar mutane.
Jami’in hulda da jama’a na Civil Defence, Mista Emeka Peters Okwechime, wanda ya bayyana haka a shelkwatar rundunar, Asaba, ya ce, rundunar ta samu gagarumar nasara wajen yaki da miyagun ayyuka a jihar, cikin watanni shida.
Ya ce, a cikin watanni shida da suka gabata, mun kama sama da mutane 42 da ake zargi da laifuka daban-daban da suka hada da harka kan haramtattun albarkatun man fetur, fasa bututun mai, satar danyen mai, garkuwa da mutane, safarar mutane, lalata da yara da kuma zamba.
Ya ce, a watan Mayun bana, kimanin mutane 8 ne aka gurfanar da su a gaban kuliya tare da yanke musu hukunci, yayin da ake tuhumar wasu da laifin zamba da sata.