Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC, ta cafke wani direban bas da ake zargi da safarar bututun danyen mai da aka lalata.
An ce bututun na kamfanin mai na Nigeria Agip Oil da ke Rivers ne.
Mukaddashin kwamandan NSCDC a Ribas, DC Claire Okpo, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal ranar Alhamis.
Sanarwar ta samu sa hannun mai magana da yawun rundunar, DSC Olufemi Ayodele.
Okpo ya ce, an kama mutumin da ake zargin a kan titin Mbiama na hanyar Gabas zuwa Yamma a karamar hukumar Ahoada.
Ya ce, tawagar jami’an tsaron kan iyakokin NSCDC ne suka kama shi.
“An kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake jigilar bututun mai da aka lalata a cikin wata motar Toyota bas mai lamba: Anambra NSH 252 YY.
“Bincike na farko ya nuna cewa, wanda ake zargin ya tattauna kan kudi kusan Naira 320,000 na bututun mai amma ya biya Naira 250,000.
“Wanda ake zargin wanda har yanzu mai laifin na hannun sa, za a tuhume shi da laifin yin lalata da kamfanin mai na Najeriya Agip ba bisa ka’ida ba, hada baki da kuma zagon kasa ga wasu muhimman kadarorin kasa,” in ji ta.