Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NPFL), ta ci tarar ƙungiyar Katsina United tara kuɗi, bisa samun ɗan wasan ta da sanya riga da rubutun lamba da aka yi da hannu.
An samu Katsina United da yin watsi da ka’idar a wasan da suka yi da Sporting Lagos a wasan mako na 11.
An umurci kungiyar Katsina United da ta biya Naira miliyan 1, domin nuna rashin dacewa da sunan dan wasan da lambarsa ba tare da ya dace ba, yayin da Manajan ƙungiyar, Masudu Lawal ya samu hukuncin dakatar da shi na tsawon shekara daya daga duk wasu ayyukan NPFL saboda rashin da’a.