Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya yi zargin cewa an yi magudi a zaben majalisar dokokin jihar Kano da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata inda jamâiyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ke mulki.
Lawan, wanda kwanan nan ya kammala zaman gidan yari na shekaru biyar bisa samunsa da laifin cin hanci, ya zargi jamâiyyar NNPP da yin ârashin adalciâ a mazabar Bagwai/Shanono da Ghari/Tsanyawa a wani sakon da ya rubuta a Facebook.
Tsohon dan majalisar wanda ya taba wakiltar Bagwai/Shanono a majalisar ya godewa magoya bayan jamâiyyar All Progressives Congress (APC) bisa abin da ya bayyana a matsayin sadaukarwar da suka yi a lokacin zaben.
“Hakika kun yi kokari da sadaukarwa, tare da girmama kiran ku fito ku kada kuri’a kamar yadda aka saba, amma da ikon Allah, kowa ya shaida rashin adalcin da jam’iyyar adawa mai mulki a jihar Kano ta yi mana a lokacin wannan zaben fid da gwani,” in ji Lawan.
Ya ci gaba da cewa, an wawure waâadin jamâiyyar APC, kuma ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, yana mai tabbatar musu da cewa jamâiyyar za ta bibiyi hanyoyin doka da na siyasa don kalubalantar sakamakon.
“Da yardar Allah, nan ba da jimawa ba za mu dauki matakan da suka dace, Allah Ya saka wa magoya bayanmu da yawa saboda soyayya da amincin da kuke ci gaba da nuna mana ba dare ba rana,” in ji shi.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa âyan takarar jamâiyyar NNPP ne suka lashe zaben mazabu biyu, amma jamâiyyar APC ta ki amincewa da sakamakon zaben.