fidelitybank

NNPP ta lashe zaɓen cike gurbi a Kano

Date:

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ayyana Dr Alhassan Zakariya Ishaq na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ranar Asabar a mazabar Kura/Garun Mallam da ke Kano.

Jami’in zabe na jihar Farfesa Shehu Musa Galadanchi ya bayyana cewa Ishaq na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 37,262 inda ya doke Musa Hayatu Daurawar na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wanda ya samu kuri’u 30,803.

Idan ba a manta ba kotun daukaka kara ta umurci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 20 da ke mazabar Kura/Garun Malam a jihar Kano.

Hakazalika, INEC, ta ayyana Bello Muhammad Butu-Butu na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ranar Asabar a mazabar Rimin Gado/Tofa.

Jami’in da ya lashe zaben Farfesa Ibrahim Tajo Suraj ya kuma bayyana cewa Bello Muhammad Butu-Butu na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 31,135 inda ya doke abokin hamayyar sa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wanda ya samu kuri’u 25,577.

Kotun daukaka kara ta kuma umurci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfuna 33 da ke mazabar Rimin Gado/Tofa.

taraba news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp