Sakataren jam’iyyar, NNPP, Oginni Olaposi Sunday, ya shaidawa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar a zaben 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso, cewa umurnin kotu da ya karbo ba zai kare shi daga gayyatar EFCC ba.
Oginni, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abeokuta a jihar Ogun.
Ya ce, girman cin hanci da rashawa da gwamnatocin baya da kuma ‘yan siyasa suka aikata a fadin kasar nan, ba a taba ganin irinsa ba, wanda ya sanya dimokuradiyyar kasar nan ta zama rauni tare da jefa ta cikin kangin talauci.
Sakatarenta na kasa, Kwamared Oginni Olaposi Sunday, ya bukaci hukumar EFCC ta binciki Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da wasu jami’an jam’iyyar kan kudaden da jam’iyyar ta karba daga kudin sayar da fom din tsayawa takara da kuma kudaden yakin neman zabe 2023.