Shugaban jam’iyyar New Nigeria People Party (NNPP) na kasa, Farfesa Alkali Ahmed Rufa’i, Alkali a jiya ya caccaki jam’iyyar APC kan neman dan takararta na shugaban kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso ya dawo jam’iyyarsu.
Alkali ya yi Allah-wadai da wata sanarwa da mataimakin sakataren yada labaran jamâiyyar APC na kasa Yakubu Ajaka ya yi kira ga Sanata Rabiâu Kwankwaso da ya koma APC saboda yana da damar zama shugaban kasa a dandalin jamâiyyar a nan gaba.
Sai dai Alkali a wata sanarwa da ya sanyawa hannu jiya a Abuja, ya ce irin wannan tunanin kamar na wani ne da ya nutse yana neman tallafi.
Ya ce, da Ajaka ya yi nazari kan halin da alâummar kasar ke ciki da ya lura da yadda âyaâyan jamâiyyar APC ke ficewa a halin yanzu da kuma na sauran jamâiyyu zuwa NNPP.